Isa ga babban shafi
Italiya

EU ta jinjina wa Majalisar Italiya

Hukumar kungiyar Tarayyar Turai ta jinjinawa ‘yan Majalisar dattawan kasar Italiya dangane da matakin da suka dauka na ci gaba da goyon bayan gwamnatin kasar karkashin jagorancin Enrico Letta.

Majalisar kasar Italiya
Majalisar kasar Italiya REUTERS/Remo Casilli
Talla

Shugaban hukumar kungiyar ta Tarayyar Turai Jose Manuel Barroso, wanda ke mayar da martani dangane da matakin ci gaba da bai wa gwamnatin Italiya goyon baya da Majalisar kasar ta yi, ya ce a halin da ake ciki, ba a bukatar tattalin arzikin kasar ta Italiya ya sake fadawa a cikin wani mummunan yanayi.

Barroso ya ci gaba da cewa kwanciyar hankali a fagen siyasar kowace kasa, wani abu ne da zai taimaka wajen kare tattalin arzikinta, saboda haka kuri’ar da ‘Yan majalisar suka jefa domin bai wa Firaminista Enrico Letta damar ci gaba da jagorantar gwamnatin kasar, wata dama ce a gare shi domin ci gaba da aiwatar da sauye-sauye na siyasa da kuma na tattalin arziki.

Shugaban na hukumar kungiyar Tarayyar Turai, ya ce matakin na majalisa, wani abin marhabin ne ba wai ga kasar Italiya kawai ba, har ma ga sauran kasashe da ke amfani da takardar kudi ta Euro.

A lokacin da aka zo jefa kuri’ar dangane da batun yunkurin kifar da gwamnatin a jiya laraba, Enrico Letta ya samu kuri’u 235 da ke goyon bayan ci gaba da rike mukaminsa, yayin da wasu ‘yan majalisa 70 suka nuna adawarsu a gare shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.