An shiga yajin aikin gama-gari da zanga-zanga a Girka

Kungiyoyin Kwadago a kasar Girka, sun kira yajin aikin gama gari, sakamakon ci gaba da matsin lambar da Fira ministan kasar Lucas Papademos ke fuskanta daga kasashen Turai, domin kara tsuke bakin aljihun gwamnati.
Akalla mutane 5,000 suka shiga zanga-zangar da aka yi jiya, domin adawa da matakan tsuke bakin aljihun, duk da ruwan sama da dussar kankarar da kasar ke fama da shi.
A yau Talata, ana sa ran jam’iyyun Hadaka da suka samar da Lucas Papademos zasu gana bayan samun cikas a zaman shugabannin jam’iyyun a jiya Litinin.
Ministan kudin kasar Girka ya zargi samun gazawar Jam’iyyun siyasa domin cim ma matsaya a yarjejeniyar kasar da kasashen Turai a hukumar Bada Lamuni.
Yanzu haka kawai matsin labba da kasar Girka ke fuskanta daga Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy da takwararsa ta Jamus Angela Merkel.
Merkel ta Jamus tace babu wani Tallafi da Girka zata samu daga kasashen Turai domin warware matsalarta har sai ta cim ma yarjejeniya da Tarayyar Turai da bankin ECB da hukumar Lamuni IMF game da tsuke bakin aljihu.

Delicious
Digg
Facebook
Twitter
Yahoo!
Technorati




Ra'ayoyi
Bada ra'ayi kan wannan magana