Turai

Syndicate contentTURAI
Wani taron shugabannin Jam'iyyun Siyasar kasar Girka
16/05/2012 - Girka

Akwai alamun sake gudanar da zabe a Girka

Kasar Girka ta kama hanyar zuwa wani sabon zaben ‘Yan Majalisu, saboda yunkurin kafa gwamnati ya ci tura, tsakanin Jam’iyyun siyasar kasar.

Tsohon shugaban hukumar bada Lamuni ta duniya Dominique Strauss-Kahn
16/05/2012 - Amurka-Faransa

Strauss-Kahn ya shigar da kara domin kalubalantar Nafisatou Diallo

Tsohon Shugaban Hukumar Bada lamuni ta Duniya, Dominique Strauss Kahn, ya shigar da kara a kotu inda yake bukatar Nafisatou Diallo, matar da ta yi masa zargin yunkurin yi mata fyade a New York, ta biya shi Dala miliyan guda, saboda bata masa suna.

Angela Merkel da François Hollande,a lokacin da suke ganawa a birnin à Berlin, bayan rantsar da Hollande matsayin sabon shugaban kasa
16/05/2012 - Faransa-Jamus

Hollande da Merkel sun yi alkawalin yin aiki tare don ci gaban Turai

Shugaban Kasar Faransa, Francois Hollande, tare da takwararsa ta kasar Jamus, Angela Merkel, sun yi alkawarin aiki tare, don ganin sun magance matsalolin da ke addabar kudin euro da kuma tattalin arzikin Turai.

Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy
15/05/2012 - Faransa

Sarkozy ya zama tsohon shugaban kasar Faransa

Yanzu Haka Nicolas Sarkozy, ya zama tsohon shugaban kasar Faransa, bayan rantsar da Hollande abinda ya kawo karshen mulkinsa na shekaru biyar da ‘Yan Faransa da dama suka yi ta korafi akai.

Sabon Shugaban Faransa François Hollande tare da Nicolas Sarkozy mai barin gado a fadar Elysee
15/05/2012 - Faransa

Hollande ya karbi ragamar shugabancin Faransa

Mai ra’ayin gurguzu, Francois Hollande ya karbi ranstuwar shugabancin Faransa tare da bayyana fatar samar da sauyi a kasar da Nahiyar Turai. Ana sa ran Sabon shugaban zai zabi Fira Ministan kafin ya nufi zuwa kasar Jamus don tattaunawa da Angela Merkel.

Alexis Tsipras, Shugaban Jan'iyyar  Syriza,  a lokacin da yake ganawa da magoya bayan shi bayan kammala zabe
14/05/2012 - Girka

Yunkurin kafa gwamnatin hadin gwiwa a Girka ya gamu da cikas

Yunkurin kafa gwamnatin hadin gwiwa a kasar Girka ya gamu da cikas bayan Jam’iyyar Syriza ta yi barazanar hada kai da sauran jam’iyyun siyasar kasar.

11/05/2012 - Turai

Kungiyar tarayyar Turai zata dauki wani sabon matakin ladabtarwa kan kasar Syriya

A ranar litanin mai zuwa ne, kungiyar tarayyar Turai zata dauki wani sabon matakin ladabtarwa kan kasar Syriya, tare da karbe kaddarorin wasu kamfanoni 2, da kuma wasu mutane 3 wadanda ake ganin suna tallafawa gwamnatin Bashar al-Assad da kudade, kamar yadda majiyar diflomasiyar kungiyar ta sanar a yau juma’a.

L'Etat espagnol sera actionnaire de Bankia a hauteur de 45%.
11/05/2012 - Spain

Gwamnatin kasar Spaniya ta dauki wasu sabin matakan tafiyar da bankunan kasar

Gwamnatin kasar Spain a yau juma’a ta amince da wani sabon shirin tafiyar da bankunan kasar da suka fi karkata kan sashen gidaje, inda aka umarci bankunan da su bayyana sakamakon ayukansu, da kuma umartarsu da samar da wani sabon shiri na kimanin Euro miliyan dubu 30 nan gaba.

Le Premier ministre français François Fillon le 23 avril 2012.
10/05/2012 - Fransa

Fra Ministan Fransa Francois Fillon ya gabatar da murabus din gwamnatinsa

A yau alhamis Fra Ministan kasar Fransa Francois Fillon ya gabatar da murabus din gwamnatinsa, wace zata ci gaba da tafiyar da wasu muhimman ayuka kafin zababben shugaban kasar Francois Hollande ya fara aiki a ranar talata mai zuwa, inda zai nada wata sabuwar gwamnati.

Shugaban Rasha Vladmir Putin
10/05/2012 - Rasha-Amurka

Obama ya taya Putin murnar sake zama shugaban Rasha

Ta Wayar Salula, Shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya taya shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin murnar sake zama shugaba a karo na uku, bayan kwashe lokaci shugabannin biyu suna adawa da juna. Sai dai Putin yace ba zai samu damar halartar taron kasashen G8 da za’a gudanar a Amurka.

François Hollande tare da Nicolas Sarkoz a ranar 8 ga watan Mayu lokacin da ake bukin tuna yakin Duniya na Biyu a birnin Paris
09/05/2012 - Faransa

Hollande da Sarkozy sun yi kafada a bukin tuna Yakin Duniya

Shugaba mai jiran gado a kasar faransa, Francois Hollande da shugaban kasar mai barin gado, Nicolas Sarkozy a jiya talata sun tsaya kafada da kafada a wani taron tunawa da yakin duniya na biyu kwana uku kacal bayan zaben da aka gudanar lahadin da ta gabata.

Alexis Tsipras Dan Jam'iyyar Syriza  a kasar Girka
09/05/2012 - Girka-EU-IMF

Girka zata yi watsi da matakan tsuke bakin Aljihun Gwamnati

Shugaban Jam’iyyar Syriza ta kasar Girka, Alexis Tsipras, ya yi alkawarin soke tallafin kasashen Turai da Hukumar bada Lamuni ta Duniya tare da yin watsi da shirin tsuke bakin aljihu idan ya kafa Gwamnati. Yanzu haka Jam’iyyar Syriza ta fara tattaunawa da sauran Jam’iyyu domin kafa gwamnatin hadin gwiwa.

Sabon Shugaban kasar Faransa François Hollande a tsakiya da  Eva Joly da Cécile Duflot, a lokacin da suke taya shi murna
08/05/2012 - Faransa

Kalubalen Matsalar Tattalin arzikin Turai zai hanawa Hollande hutu

Kwanaki bayan samun nasarar shi a zaben shugaban kasar Faransa, François Hollande zai fuskanci jerin bukatun Faransawa kafin kama aiki a fadar shugaban kasa. Babban kalubalen da ke gaban sabon Shugaban shi ne daidaita matsalar tattalin arzikin Faransa.

'Yan Sandan kasar Rasha suna kokarin cafke wani daga cikin gungun masu zanga-zangar adawa da Putin a jajibirin ratsar da shi a Moscow
07/05/2012 - Rasha

An rantsar da Putin matsayin sabon Shugaban Kasar Rasha

Vladimir Putin ya karbi rantsuwar shugabancin kasar Rasha karo na uku bayan an yi taho mu gama tsakanin Jami’an tsaro da masu zanga-zangar adawa da gwamnatin shi. Putin ya karbi rantsuwar kare ‘Yancin kasar Rasha da mutanenta Bayan ya rungume kundin tsarin mulkin kasar.

François Hollande Sabon shugaban kasar Faransa wanda ya kada Nicolas Sarkozy
07/05/2012 - Faransa

Hollande ne sabon shugaban Faransa bayan ya kada Sarkozy

Dan takarar Jam’iyyar Gurguzu ta Socialist François Hollande ya kada shugaban kasa mai ci Nicolas Sarkozy a zaben shugaban kasar Faransa zagaye na biyu. Hollande shi ne Mutum na Farko da ya lashe zaben shugaban kasa karkashin Jam’iyyar Gurguzu tun zamanin François Mitterrand a shekarar 1988.

Shugaban Rasha, Dmitry Medvedev da  Vladimir Poutine da  Pyotr Biryukov a birnin Moscow lokacin bukin ranar ma'aikata
04/05/2012 - Rasha

Rasha ta amince a yi zanga-zanga jajibirin rantsar da Putin

Hukumomin kasar Rasha, a karon farko sun bada dama ga ‘yan adawa domin gudanar da gangami a tsakiyar birnin Moscow. Wannan kuma na zuwa ne kwana daya kamin kaddamar da shugaba Vladmir Putin a wa’adi na uku.

François Hollande, Dan takarar Shugaban kasa mai hamayya da Sarkozy  karkashin Jam'iyyar gurguzu ta socialist a lokacin da yake tattaunawa da wakilan Rediyo Faransa RFI da Gidan Telebijin na France 24
04/05/2012 - Faransa

Sarkozy ya zubar da mutuncin Faransa, inji Hollande

A wata hira ta musamman da François Hollande ya yi da RFI da France 24, dan takarar shugaban kasar Faransa yace ya yaba da kokarin shi a muhawarar da ya yi da Sarkozy tare da sukar gwamnatin Sarkozy ta raba Faransawa.

03/05/2012 - Turai-Guinee Bissau

kungiyar tarayyar turai ta ce zata kakabawa sojojin da suka kifar da gwamnatin kasar Guine Bissau takunkumi

Kunghiyar Tarayyar Turai ta kakabawa Jagororin juyin mulki na kasar Guinea Bissau takunkumin hana su sukuni, bayaga jerin takunkumin da Kungiyar kasashen yammacin Africa suka riga suka kakaba masu.

Dandalin Muhawarar da aka gudanar tsakanin Hollande da Sarkozy
03/05/2012 - Faransa

Sarkozy da Hollande sun tabka muhawara tare da sukar juna

Shugaban Kasar Faransa, Nicolas Sarkozy, da abokin adawarsa, Francois Hollande, sun yi musayar kalamai marasa dadi a mahawarar karshe da suka gudanar yammcin jiya, kafin zabe zagaye na biyu a ...

Wasu Jaridun kasar Faransa
02/05/2012 - Zaben Faransa

Sharhin Jaridun Faransa a yau

Hankalin Jaidun Faransa a yau ya rabu gida biyu domin wasu sun mayar da hankali ne akan yakin neman zaben ‘Yan siyasa da aka gudanar a jiya ranar bukin ma’aikata, wasu kuma jaridun sun mayar da hankali ne akan muhawarar da za’a gudanar a yau tsakanin Sarkozy da Hollande a kafar Telebijin.

Close