Urgent published the Laraba 08 Feberairu 2012
An saki ma’aikatan China a Sudan
Yan Tawayen Sudan sun saki wasu ma’aikata ‘Yan kasar China 29, da suka yi garkuwa da su na kwanaki goma, a Jihar kudancin Kordafan. ‘Yan Tawayen sun ce sun kama ma’aikata ne dan kare lafiyar su, sakamakon fafatawar da suke da Gwamnati.




