Kasashen Afrika na da dumbin arziki ,sai dai kuma ,su ka kassance sun fi kowa talauci a duniya.Ta bangaren Halin rayuwa ,kiwon lahiya,ilimin kimiya da dai saurensu ,kasashen sun kassance koma baya a duniya .Wanan lamari na da babban mahimmanci da a tunkareshi da idon rahama.
Nahiyar Afrika na da fadin murabadin kilomita milyon 30, da dubu dari 2 da 21 da dari 5 da 31 .Ta kwashi kishi 6 cikin dari na fadin duniya.A yanzu haka nahiyar na da al’ummar da yawanta yak ai milyar daya da kuma ta kassance kishi 16 da digo 14 cikin dari na yawan al’ummar duniya.