Syndicate content
Labaran jiya
Wani manomi a yankin kasar Chadi
16/05/2012 - MDD-Afrika

Sai an Magance Yunwa kafin a samu ci gaba a Afrika, Inji MDD

Hukumar Ci gaba ta Majalisar Dinkin Duniya, tace dole sai kasashen Afrika sun magance matsalar yunwa da ke addabar kasashe 27 a nahiyar kafin kasancewa matsayin Yankin da ya samu ci gaba.

Dan wasan Manchester United Rio Ferdinand
16/05/2012 - Ingila

Hodgson ya ajiye Ferdinand a tawagar Ingila zuwa gasar Turai

sabon kocin ‘Yan wasan Ingila, Roy Hodgson ya ajiye Rio Ferdinand cikin tawagar shi da zasu haska a gasar cin kofin Turai a kasashen Ukraine da Poland.

Francois Bocande Tsohon Dan wasan Senegal wanda ya mutu yana da shekaru 54
16/05/2012 - Senegal

Dubban mutanen Senegal sun karrama Bocande

A kasar Senegal daruruwan mutane ne suka yi gangami a babban filin wasan kwallon kafa a Dakar, domin karrama fitaccen dan wasan kwallon kafar kasar Francois Bocande wanda ya mutu a ranar 7 ga watan Mayu a kasar Faransa.

Gungun mata da Amaren da aka daurawa aure a Kano
16/05/2012 - Najeriya

Hisbah ta daura auren Zawarawa 100 a Kano

Hukumar Hisbah a Jihar Kano, ta daura wa Zawarawa 100 aure cikin 1,000 da aka shirya yi, dan magance mace macen aure a Jahar.

Wani taron shugabannin Jam'iyyun Siyasar kasar Girka
16/05/2012 - Girka

Akwai alamun sake gudanar da zabe a Girka

Kasar Girka ta kama hanyar zuwa wani sabon zaben ‘Yan Majalisu, saboda yunkurin kafa gwamnati ya ci tura, tsakanin Jam’iyyun siyasar kasar.

Tsohon shugaban hukumar bada Lamuni ta duniya Dominique Strauss-Kahn
16/05/2012 - Amurka-Faransa

Strauss-Kahn ya shigar da kara domin kalubalantar Nafisatou Diallo

Tsohon Shugaban Hukumar Bada lamuni ta Duniya, Dominique Strauss Kahn, ya shigar da kara a kotu inda yake bukatar Nafisatou Diallo, matar da ta yi masa zargin yunkurin yi mata fyade a New York, ta biya shi Dala miliyan guda, saboda bata masa suna.

Ratko Mladic a zauren kotun duniya lokacin sauraren karar shi a ranar 3 Yuni 2011.
16/05/2012 - Serbia-ICC

Sauraren karar Kwamandan Serbia, Ratko Mladic a gaban kotu

Tsohon kwamandan Serbia, Janar Ratko Mladic, ya gurfana a gaban kotun Duniya a birnin Hague domin fuskantar zargi 11 na laifukan yaki da kisan kare dangi da keta hakkin bil’adama a yakin Bosnia a shekarar 1992-95.

Angela Merkel da François Hollande,a lokacin da suke ganawa a birnin à Berlin, bayan rantsar da Hollande matsayin sabon shugaban kasa
16/05/2012 - Faransa-Jamus

Hollande da Merkel sun yi alkawalin yin aiki tare don ci gaban Turai

Shugaban Kasar Faransa, Francois Hollande, tare da takwararsa ta kasar Jamus, Angela Merkel, sun yi alkawarin aiki tare, don ganin sun magance matsalolin da ke addabar kudin euro da kuma tattalin arzikin Turai.

Close