Nijar

Syndicate contentNIJAR
kamfanin Areva, mallakar kasar Faransa, da ke hako ma’adinin uranium a Yankin Arlit a Jamhuriyyar Nijar
15/05/2012 - Nijar-Faransa

Wata kungiyar Farin kaya ta nemi kamfani Areva ya biya ‘Yan Nijar diyya

Wata Kungiyar fararen hula a Jamhuriyar Nijar, ta bukaci kamfanin Areva, mallakar kasar Faransa, da ke hako ma’adinin uranium a kasar, biyan kudaden Diyya ga ‘Yan Nijar dai dai da yadda Kamfanin ke biyan Faransawan da suka mutu.

Garken Rakuma suna sha ruwa a gabar Tabkin Chadi da ke kewaye da tsaunuka
09/05/2012 - Nijar-Najeriya-Chadi

Kasashen raya tabkin Chadi zasu samar da dakarun hadin gwiwa don yaki da Ta’addanci

Manyan Jami’an tsaron kasashen da ke raya tafkin Chadi, sun gudanar da taro a Jamhuriyar Nijar, don nazarin hanyoyin da zasu dakile safarar makamai da kuma ayyukan ta’adanci domin samun ci gaban kasashensu.

Jerin Mata masu shayarwa a Nijar suna jiran Likita
09/05/2012 - Nijar-Save the Children

Nijar ta yi watsi da rahoton Save The Children akan Mata

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta yi watsi da rahotan kungiyar agaji ta Save the Children, wanda yace mata na fama da tsananin wahala wajen haihuwa da kuma renon kananan yara, abinda ya sa kasar ta zama ta karshe a mizanin kasashen duniya 165.

Matan kasar Afghanistan a lokacin gudanar da bukin ranar mata a yankin Ghazni a ranar 8 ga watan Maris
08/05/2012 - Lafiya

Kasar Norway ne iyaye mata suka fi shan dadi amma a Nijar suka fi shan wahala

A wani sabon Rahoto game da halin rayuwar iyaye mata da hukumar kare lafiyar kananan yara ta fitar, ya nuna Nijar ce kasar da iyaye Mata ke shan wahala bayan maye gurbin kasar Afghanistan a karon farko. Kasar Norway ce a matsayin kasa ta farko da iyaye Mata ke shan dadi a jerin kasashe 165 da aka kwatanta rayuwarsu.

Shugaban Kungiyar Boko Haram a Najeriya Iman Abubakar Shekau a sakonsa ga shugaba Jonathan.
01/05/2012 - Chad-Najeriya

Gwamnatin Chadi ta nemi samar da dakarun hadin kai don yaki da Boko Haram

Gwamnatin kasar Chadi ta yi kiran kasashen 16 a kungiyar raya tafkin Chadi domin samar da dakarun hadin kai don yaki da ‘Yan kungiyar Boko Haram da ke barazana ga sha'anin tsaro a Najeriya da makwabtanta.

Mahamadou Issoufou, Président de la République du Niger
30/04/2012 - NGER-LIBYE-FRANCE

Bashir Saleh tsohon na hannu damar Konal Kaddafi baya dauke da Fasfon kasar Niger...

Bashir Saleh tsohon jami’in gwamnatin kasar Libiya, wanda ya kasance na kusa ga tsohon shugaban kasar Ma’amar Kaddafi, wanda aka ambata sunansa a cikin zargin daukar nauyin yakin neman ...

Saurari ra'ayinka game da matsalar Mutuwar Aure a kasar Hausa
27/04/2012 - Tattaunawa

Saurari ra'ayinka game da matsalar Mutuwar Aure a kasar Hausa

Akwai matsalar mace-macen aure da ake samu a kasar Hausa, kuma mutuwar Aure ba wani sabon abu bane tsakanin al'ummar hausawa.

Wani sanye da Rawani a yankin Timbuktu a kasar Mali
19/04/2012 - Afrika-Bankin Duniya

Bankin Duniya yace an samu ci gaba a kasashen Yamma da Sahara

Babban Bankin Duniya yace tattalin Arzikin kasashen yammacin Afrika ya samu ci gaba bana. Wannan na zuwa ne saboda samun rangwame ga farashin kaya da yawaitar hannayen jari da hako ma’adanai da suka kawar da raunin fitar da kaya zuwa waje.

Shugaban Niger, Mahamadou Issoufou.
02/04/2012 - Nijar

Gwamnatin Niger ta sallami wasu ministoci 3

Gwamnatin jamahuriyar Niger ta bayar da sanarwar sallamar wasu Ministoci 3, tare da bayar da sanarwar nadi wadanda za su maye gurbin su.

Matsalar Hunturu ga Lafiyar Dan Adam
27/03/2012 - Lafiya

Matsalar Hunturu ga Lafiyar Dan Adam

Shirin Lafiya Jari ya diba matsalar hunturu ga Lafiyar al'umma a kasashen Afrika tare da tattaunawa da Likita wanda ya yi bayani dangane da yadda mutum zai kare lafiyar shi ga kamuwa da cutar ...

Babban kwamandan 'Yan Tawayen MNJ yana rangadin dakarun shi a yankin arewacin Nijar
22/03/2012 - EU-Nijar

Kasashen Turai zasu bada horo ga Sojin Nijar don yaki da Ta'addanci

Kungiyar kasashen Turai ta EU zata amince da kudirin tura tawagar da zata horar da sojin Jamhuriyar Nijar, don fuskantar kalubalen yaki da ta’adanci da ke yaduwa a iyakokin kasar sanadiyar rikicin kasar Libya da Mali masu makwabtaka da Nijar.

21/03/2012 - Janhuriyar Nijar

Mahukumtan kasar Mauritaniya sun maka tsohon shugaban kungiyar yan tawayen MNJ a kurkuku

Aghali Alambo,wani tsowo shuganban yan tawaye MNJ ne, a Jamhuriyar Niger na tsaka mai wuya, bayan da hukumomin kasar ke tuwuma sa da alaka da yan ta’ada.

Kokuwar gargajiyar Nijar a Maradi
12/03/2012 - Wasanni

Kokuwar gargajiyar Nijar a Maradi

Shirin ya diba kokuwar gargajiyar Jamhuriyyar Nijar da aka kammala a Jahar Maradi inda Laminou Mai Dabba na Agadez ya lashe Takobin Kokuwar a bana bayan ya karba hannun Ummaru Bindigou na Maradi.

Laminou mai Dabba na Agadez ya zama sarkin Kokuwar Nijar na 2012
05/03/2012 - Wasanni

Laminou mai Dabba na Agadez ya zama sarkin Kokuwar Nijar na 2012

An kammala gasae kokuwar gargajiyar kasar Janhuriyar Nijar na wannan shekara ta 2012, bayan samu nasara yayin wasan karshe da aka ranar Lahadi hudu ga wan Febrairu.

Saadi Gaddafi
27/02/2012 - Janhuriyar Nijar

Janhuriyar Nijar ta gargadi 'yan kasar kan zuwa Libya

Gwamnatin kasar Janhuriyar Nijar ta gargadi 'yan kasar da su kaucewa zuwa kasar Libya, saboda fargabar kai musu hari daga 'yan Tawayen kasar

'Yan wasan Kokuwa a kasar Jamhuriyyar Nijar gasar da aka gudanar a Zinder a bara.
24/02/2012 - Kokuwa

Za’a bude gasar kokuwa a Maradi

A yau ne za’a bude gasar kokuwa a Jamhuriyyar Nijar a birnin Maradi, bayan fara gasar a shekarar 1975 a birnin Tawa, kuma tun a lokacin ne ake gudanar da gasar ta kokuwa duk shekara. Yanzu haka an gudanar da gasar sau 31 bayan kammala gasar a bara a birnin Tliberi.

Wasu 'Yan gudun Hijira da ke kaura daga kasar Somalia sanadiyar rikicin gwamnati da kungiyar Al shabab
21/02/2012 - Mali-Nijar-Burkina

Daruruwan mutane suke gudun hijira daga Mali

Akalla ‘Yan gudun hijira 35,000 suka tsere daga kasar Mali zuwa kasashen Burkina Faso da Nijar, don samun mafaka sanadiyar rikicin da ake ci gaba da gudanarwa tsakanin ‘Yan tawayen Tuareg da dakarun Gwamnati.

Matsalolin Nijar da Najeriya a kwallon kafa
20/02/2012 - Wasanni

Matsalolin Nijar da Najeriya a kwallon kafa

A cikin shirin, mun diba irin matsalolin da suka shafi Tawagar ‘Yan wasan Mena a gasar cin kofin Åfrika da aka kammala a kasashen Gabon da Equatorial Guinea da irin matsalolin da suka shafi kwallon kafa a Najeriya da sabbin sauye sauye da kasar ke yi domin kaucewa bacin rana.

Taswairar yankin kudu da Sahara
16/02/2012 - MDD-EU-Sahel

MDD ta bukaci Tallafin gaggawa domin magance Yunwa a yankin kudu da Sahara

Shugabannin kwamitin Tallafi na Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Turai sun nemi kasashen duniya bayar da tallafin gaggawa, domin shawo kan matsalar yunwa da ke addabar yankin Sahel na yammacin Afrika, inda suka bayyana cewa ana bukatar kudi Dalar Amurka miliyan 725 a bana.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a lokacin da yake zatawa da kamfanin Dillacin Labaran Reuters a fadar shugaban kasa.
16/02/2012 - ECOWAS

Shugabannin ECOWAS zasu gudanar da Taronsu a Abuja

Shugabanin kasashen Afrika ta Yamma, na kungiyar ECOWAS, zasu gudanar da taronsu a Abuja, inda ake saran zasu zabi sabon shugaba, saboda kawo karshen wa’adin Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya.

Close