Isa ga babban shafi
Nigeria

Ahmed Mu'azu ya sauka daga shugabancin PDP a Nigeria

Yau Laraba, Shugaban Jam'iyyar PDP a Nigeria, Alhaji Ahmed Adamu Mu'azu ya ajiye aikinsa. Cikin takardar ajiye aiki da tsohon shugaban ya aike jam'iyyar ta PDP, Mu'azu yace rashin lafiya ne ya sa shi yin murabus, don ya samu damar neman magani.Dama Adamu Mu'azu ya dade yana takun saka da wasu 'ya 'yan jam'iyyar ta PDP, musamman jami'an fadar shugaban kasa mai barin gado Goodluck Jonathan, da jami'in ofishin yaki neman zabensa, da suke zargin tsohon shugaban, da yiwa PDP zagon kasa, a zaben shugabancin kasar da aka yi a watan Maris da ya gabata, inda Shugaban Jonathan, karkashin jam'iyyar ta PDP ya sha kaye a hannun Muhammadu Buhari na APC.

Mai Dakin Shugaban Nigeria mai barin gado Patience Goodluck Jonathan, Goodluck Jonathan, shugaban jam'iyyar PDP Ahmed Mu'azu, da Cif Edwin Clarck a Yanagoa
Mai Dakin Shugaban Nigeria mai barin gado Patience Goodluck Jonathan, Goodluck Jonathan, shugaban jam'iyyar PDP Ahmed Mu'azu, da Cif Edwin Clarck a Yanagoa REUTERS/Stringer
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.