Boko Haram: Nijar ta haramta sana’ar Kifi a Diffa
Daruruwan ma su sana’ar Kifi daga Diffa zuwa Najeriya sun shiga matsalar zaman kashe wando, bayan da hukumomin Jamhuriyar Nijar suka haramta masu sana’ar bisa zargin cewa wasu daga cikinsu na shigarwa ‘yan Boko Haram da makamai da abinci.
Wallafawa ranar:
Mataimakin magajin garin Maini a Jihar ta Diffa Alhaji Gremah Bukar, ya roki jama’a da su bai wa hukumomi hadin kai domin tabbatar da tsaro a Jihar da ke fama da barazanar Boko Haram.
Alhaji Gremah ya ce cikin masu sana’ar kifin akwai mugaye a cikinsu wadanda ke hada baki da Boko Haram.
Ana kuma zargin ‘yan kasuwan da biyan haraji ga kungiyar Boko Haram wadanda ke yi ma su barazanar kwace kifin don sayarwa su samu kudade.
A makon jiya jirgin yakin Nijar ya kai hari kan tawagar ‘yan kasuwar da ke fataucin kifi zuwa Najeriya
Tuni hukumomin Nijar suka kafa dokar ta-baci a yankin Diffa domin yakar Mayakan Boko Haram na Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu