Mutane 37 suka mutu a hare haren Kano da Potiskum
Akalla mutane 37 aka tabbatar da mutuwarsu a hare haren kunar bakin wake guda biyu da aka kai a tashar mota a biranen Kano da Potiskum a arewacin Najeriya. cikin sa’I’o kalilan ne aka kai hare haren a ranar Laraba a yayin da ya rage saura makwanni biyar a gudanar da babban zabe a kasar.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Mutane 17 suka mutu a harin farko da aka kai a tashar Motar Dan-Borno a garin Potiskum, sama da 30 ne kuma suka samu rauni.
Bayan sa’o’I kalilan ne kuma wasu ‘yan kunar bakin wake guda biyu suka tayar da bom a tashar motar Kano Line.
Wakilin RFI a Kano Abubakar Issa Dandago ya ce ‘Yan kunar bakin waken sun tayar da bom din ne a cikin mota kirar Golf.
Amma rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano tace mutane 12 ne suka mutu.
Rahoton Harin kunar bakin wake a Kano Line
Wannan dai shi ne hari na farko da aka kai a Kano a 2015 bayan hare haren baya da aka kai inda aka samu hasarar rayukan mutane da dama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu