Idris da ya kera jirgi ya sake kera lemar tashi sama a Kano
Wallafawa ranar:
Kunna - 10:20
Shirin Ilimi Hasken Rayuwa ya tattauna ne game da lemar da ke tashi sama da mutum da ake kira Paramotor a turance, wanda wani matashin garin Kano Idris Ibrahim Hassan ya samar bayan ya kera jingin sama a watannin da suka gabata.
An dade dai da samar lemar da ake amfani da ita a diro daga jirgin sama wacce ake kira ‘Parachute’, daga baya ne kuma aka samar da Paramotor mai dauke da inji da fanka da kuma lemar da mutum zai rataya a baya ya tashi sama daga kasa.
Bidiyo
Shirin ya tattauna da Idris wanda ke ci gaba da aikin kere kerensa na fasahar ababen hawa da ke tashi sama. Kuma a cikin Shirin Idris ya yi bayani game da dalilin kera Paramoto da kuma amfanin shi ga al’umma.
Idris yana gudanar da ayyukan kere kerensa na fasaha da kudin aljihunsa, kuma yace babban abin da ya ke nema a yanzu shi ne tallafin daukar nauyin karatunsa a fannin kirar jiragen sama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu