Isa ga babban shafi

Kotu ta rushe zaben hukumar NFF a Najeriya

Rikicin da aka dade ana tafkawa a hukumar kwallon kafan Najeriya ta NFF ya dauki wani sabon salo, bayan da jiya Alhamis wata babbar kotun taraiyya dake Jos, ta soke zaben da aka yi wa Mr. Amaju Pinnick a matsayin shugaban hukumar. Cikin hukuncin daya yanke, alkali Ambrose Allagoa yace an yi zaben ne bayan da wata kotun tace kar a yi shi, don haka ya bayar da umarnin a koma yadda lamura suke kafin zaben, wato kenan a koma ga zaben daya samar da Chris Giwa a matsayin shugaban hukuamar ta NFF.Watakila wannan sabon rikicin yayi sanadiyyar hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA ta dakatar da Najeriya daga harkokin kwallon kafa na kasa da kasa.A halin da ake ciki kuma mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagle, Shaibu Amodu yace ba zai sauya dukkan ‘yan wasan dake taka leda a kungiyar, da Stephen Keshi ya tafi ya bari ba.Dama a kwanakin baya Amodu ya karbi ragamar kungiyar, bayan da hukumar kwallon kafan kasar ta NFF tayi waje rod da Keshi, saboda kungiyar ta gagara yin wani abin kirki, a wasannin neman shiga gasar cin kofin Africa na shekara mai zuwa, inda suka sha kashi a wasanni 2 cikin 4 da suka yi, yayin da suka yi kunnen doki a 1, suka yi nasara a wasa daya kawai. 

Wasu 'yan wasan kungiyar kwallon kafa na Najeriya, Super Eagles
Wasu 'yan wasan kungiyar kwallon kafa na Najeriya, Super Eagles AFP/Javier Soriano
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.