Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan Najeriya na kalubalantar Gwamnati kan kare batun sayen Makamai

Wani babban Lauya a tarayyar Najeriya Barrister Festus Keyamo, ya kalubalanci gwamnatin tarayyar kasar kan ikrarin da ta yi na cewar kudin da aka kama a kasar Afrka ta kudu da manufar sayen makamai mallakarta ne

facebook
Talla

Barrister Festus Keyamo, wanda ya gabatar da sanarwa ga manema labarai, ya ce yanda gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi kane-kane akan zargin cinikin Makamai ba bisa ka’ida ba da ake yiwa kungiyar Kiristocin Najeriya, bai kamata ba.

Festus Keyamo, ya ce a nashi gani babu gaskiya a ciki, kuma lura da yanda aka yi niyyar gudanar da cinikin makaman ya nuna wasu abubuwa da ake boye wa.

Na daya, cewar gwamnatin Najeriya na sane da batun. Na biyu da kuma saninta aka fitar da kudaden. Na ukku ta kuma san da batun cinikin Makaman da tsabar kudi, domin a gaggauta sayen makaman bisa wata manufa.

Keyamo ya ce idan da gaske ne cinikin na gwamnatin Najeriya ne, yaya aka yi ‘yar uwarta ma’ana gwamnatin Afrika ta kudu bata da labari.

Me yasa za’a dauki kudin gwamnatin tarayya a jirgi mai zaman kansa, ga na gwamnati ba’a saka a ciki ba, kuma ba’a hada su kudin da jami’in gwamnati ko daya ba?

Me ya sa inji Barrister gwamnatin da ta fito da tsarin rage mu’amala da kudu [cashless society] ta karya tsarin ta kwashi kudi tsuransu zuwa sayen makamai.

Me ya sa ofishin jakadancin Najeriya a Afrika ta kudun ma bai san da batun ba sai da Asiri ya tonu?

Wai ma inji Barrister, daga ina ne gwamnatin Najeriyar ta samo kudin? Kuma ta wane Banki aka fitar da su?

Barrister Festus Keyamo ya ce shi a ganinsa, wata kulalliya ce kawai ke akwai tsakanin shugaban kasar da abokinsa, Pasto Ayo Oitsejafor shugaban kungiyar Kiristoco wato CAN, wanda kuma ya ki fitowa ya nemi ahuwar ‘yan Najeriya kan wannan batu na rashin gaskiya da aka kitsa bisa karfin hali, domin sayen makaman kisan bayin Allah da basu ji ba basu gani ba.

To bayan samun wannan sakon manema labarai daga Barrister Keyamo, mun yi kokarin tuntubar Ministan watsa labarai na Najeriya Labaran Maku, domin jin irin martanin da gwamnatin kasra za ta mayarwa Barrister Keyamo da ma ‘yan Najeriya da dama musamman daga yankin Arewacin kasar, amma bai dauki Waya ba, sai dai duk lokacin da gwamnatin ta fitar da wani bayani, za mu wallafawa masu sauraro.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.