Isa ga babban shafi
Najeriya-Kamaru

Soyinka ya zargi shugaban Najeriya da kare wadanda ake zargi da hannu a Boko Haram

Fitaccen Marubucin Najeriya Farfesa Wole Syinka, ya zargi shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da kare wadanda ake zargi da daukar nauyin ayyukan kungiyar Boko Haram daga fuskantar tuhuma.A wata sanarwar da ya rabawa manema labarai a karshen mako, Soyinka daya taba lashe lambar yabo ta Nobel, yace shugaba Jonathan ya gwammace ya kare masu aikata laifufuka, cikin su harda masu daukar nauyin kungiyar Boko Haram, dan neman goyan bayansu a shirin takarar sa a zaben shugabancin kasa, a shekara mai zuwa.Farfesa Soyinka yace shi da kansa ya gudanar da bincike inda ya gano wanda ke baiwa kungiyar kudi daga Babban Bankin Najeriya, kuma binciken sa ya nuna cewa na baiwa shugaba Jonathan sunan mutumin.A bangare daya kuma kungiyar Dattawan Jihar Barno ta hannun Sakataren ta Bashir Talbari, tace tana na kan bakar ta cewar masu kai hare hare a jihar suna samun taimako daga cikin gida ne. 

Marubuci Farfesa Wole Soyinka
Marubuci Farfesa Wole Soyinka DR
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.