Isa ga babban shafi
Ilimi Hasken Rayuwa

An yi tuma-kasa a Jarabawar WAEC a Najeriya

Wallafawa ranar:

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa ya tattauna ne game da sakamakon jarabawar kammala Sakandare ta WAEC da aka fitar a Najeriya inda kuma dalibai da dama suka fadi jarabawar. shirin ya ji ta bakin wasu daliban da suka fadi jarabawar da kuma masu ruwa da tsaki a sha’anin ilimi a kasar.

Daliban Makaranta a Jahar Katsina
Daliban Makaranta a Jahar Katsina woldfolio
Talla

A makon da ya gabata ne hukumar gudanar da jarabawar kammala Sakandare ta WAEC ta fitar da sakamakon jarabawar da dalibai suka rubuta a bana, kuma dalibai da dama ne suka fadi jarabawar.

Adadin dalibai sama da Miliyan daya da dubu dari shida suka rubuta jarabawar amma daga cikin daliban, rabin Miliyan ne suka samu Credit biyar hadi da darasin Turanci da Lissafi da suka wajaba ga dalibana Najeriya. Kamar yadda hukumar ta bayyana.

Hukumar kuma tace wannan sakamakon ya fi muni fiye da faduwar jarabawa a 2012 da 2013.

Shirin ya tattauna da daliban Sakandare a Najeriya da suka fadi jarabawar tare da jin ta bakin mahukuntan kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.