Isa ga babban shafi
Amurka-Africa

Amurka tace sojanta baza suyi yaki da 'yan Boko Haram ba

Amurka tace ba zata bayar da tallafin sojojinta ba, wajen kawo karshen tashe tashen hankiulan da ke faruwa a nahiyar Africa. Mai baiwa Shugaba Obama Shawar kan harkokin tsaro Susan Rice, tace hukumomin Washinton a shirye suke su horas da masu aikin kawo zaman lafiya a nahiyar.Susan Rice, dake magana kafin taron da Shugaba Obama zai yi da wasu shugabannin nahiyar Africa su kusan 50 a ranar Litinin mai zuwa, tace Amuraka a shirye take wajen tallafawa kawayenta su fuskanci barazanar tsaron da ke gabansu.Cikin jawabin da ta gabatar Rice ta yi misala da sace mutane da tayar da Bama Bamai da Boko Haram ke yi a Nigeria, harin kasuwa da kungiyar al Shebab tayi Kenya da kuma yadda ‘yan kungiya AQIM suka karbe wasu sassan kasar Mali.Kusan dukkan shugabannin kasashen Africa ne zasu halarci taron, in banda Robert Mugabe na Zimbabwe, Omar al Bashir na Sudan da shugaban Eritrea Issaias Afeworki, da ake gani basa ga maciji da kasshen yammacin duniya.Rice tace tun lokacin da shugaba Obama ya dare shugabancin Amurka, kasar ta baiwa MDD tallafin kusan Dala Biliyon 9, don ayyukan dawo da zaman lafiya a Africa. 

Shugaban Amurka, Barack Obama
Shugaban Amurka, Barack Obama ©REUTERS/Joshua Roberts
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.