Isa ga babban shafi
Najeriya

An kwace hodar Cocaine ta fiye da Dala miliyan 7 a Nigeria

Hukumar hana fasa-kwabrin kwayoyi ta tarayyar Nigeria ta kame hodar iblis ta Cocaine a Lagos, da kudinta ya haura Dalar Amurka miliyan bakwai, da aka yi fasa-kwabrinta cikin wani jirgin ruwa daga Bolivia.Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nigeriyar ta ce an nade hodar ne cikin fakiti-fakiti na ‘Tayil’ da ake daben zamani da shi.An sami jumlar makunsai dari masu nauyin kilogiram 110 kowanne, kuma an kiyasta farashin kowane daya a kan fiye da Naira miliyan dubu daya.Dan fasa-kwabrin na nan yana amsa tambayoyi.  

Sinki-sinki na hodar Ibilis ta cocaïne.
Sinki-sinki na hodar Ibilis ta cocaïne. DEA
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.