A hirar shi da Rediyo Faransa, Mai Martaba Sarkin Gwandu mai Murabus, Manjo Mustapha Haruna Jokolo kuma Tsohon Dogarin Janar Muhammadu Buhari, yace babu wani ci gaba da shugabannin Arewa suka tsinanawa yankin bayan kwashe shekaru ‘Yan arewa na mulki a Najeriya. Jokolo yace ci gaban da gwamnatin su Sardauna suka samar a Arewa yanzu sai dai Tarihi.
Gwamnatin Najeriya tace zata girke dakarunta a kasar Guinea Bissau don taimakawa kasar komawa ga mulkin fararen hula, kamar yadda kungiyar ECOWAS ta bukata.
A yau shirin na mu zai ji ra’ayoyinku ne a akan zanga zanagar lumunar da kungiyoyin farar hula su ka ca zasu gudanar domin jinkirin da gwamnatin tarayya ke yi wajen cafke wanda a aka sami ...
KUNGIYAR likitoci ta duniya Doctors Without Borders tace fiye da yara kanana dubu dubu daya da dari 5, sun shaki gubar dalma a kauyen Bajega da ke jihar zamfara a taraiyyar Nigeria.
A wata ziyara da kai kasar Cote d’Ivoire, Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, yace kungiyar kasashen Afrika ta Yamma, ECOWAS, zata tura wata tawaga zuwa kasar Guinea Bissau don tattaunawa da sojojin kasar, domin ganin sun mayar da kundin tsarin mulki.
Manyan Jami’an tsaron kasashen da ke raya tafkin Chadi, sun gudanar da taro a Jamhuriyar Nijar, don nazarin hanyoyin da zasu dakile safarar makamai da kuma ayyukan ta’adanci domin samun ci gaban kasashensu.
Ma’aikatan Lafiya a Najeriya sun tsunduma cikin yajin aikin gama-gari, saboda kin biya musu bukatun su da Gwamnatin kasar ta yi. Wannan kuma na zuwan ne kwana daya da korar Likitoci kusan 800 da gwamnatin Lagos ta yi saboda yajin aikin da suka kwashe makwanni suna gudanarwa saboda neman karin karin albashi. Dakta Muhammed Ali Pate shi ne Ministan Lafiya kuma ya yi bayani daga bangaen gwamnati.
A wani sabon Rahoto game da halin rayuwar iyaye mata da hukumar kare lafiyar kananan yara ta fitar, ya nuna Nijar ce kasar da iyaye Mata ke shan wahala bayan maye gurbin kasar Afghanistan a karon farko. Kasar Norway ce a matsayin kasa ta farko da iyaye Mata ke shan dadi a jerin kasashe 165 da aka kwatanta rayuwarsu.
Rahotanni daga garin Potiskum dake jihar Yobe a Nigeria na cewa hankulan matasan garin ya tashi matuka sakamakon zargin da sukeyi, wa jami'an tsaron hadin guiwa dake garin, na hannu tsundum ...
Gwamnatin Jahar Flato a Najeriya ta sanar da haramta yin Acaba da babura a birnin Jos da kewaye, saboda yunkurin dakile ayyukan laifi da ake da baburan, kamar yadda ta sanar bayan taron Majalisar ...
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon ya yi bayani ne game da Rashidi Yakini tsohon dan wasan Super Eagle a Najeriya wanda Allah ya yi wa rasuwa a ranar Juma’a 4 ga watan Mayu yana da shekaru 48 bayan kwashe lokaci yana jinyar rashin lafiya.
A kalla mutane 34 ne suka rasa rayukansu a cikin wani harin Bam da aka kai a wata kasuwa dake garin Patiskum na jahar Yobe, a yankin arewacin tarayyar Nigeriya, kamar yadda majiyoyin gwamnatin jahar Yobe, da na shaidun gani da ido suka tabbatar, inda aka bayyana cewa, yawan mutane da suka rana rayukansu na iya karuwa.
Kungiyar Jama'atu Ahlus Sunnah Lidda'awati wal Jihad da aka fi sani da sunan Boko Haram a Najeriya, ta fitar da Wani hoton Bidiyo mai dauke da bayanin harin Ofishin Jaridar This Day tare da yin barazanar ci gaba da kai wasu hare hare a manyan kafafen yada labarai da ma'aikatansu a kasar.