Isa ga babban shafi

Fifa na duba yuwuwar tsaurara takunkuman da aka lafta wa Luis Rubiales

Kwamitin Fifa da ya dakatar da shugaban hukumar kwallon kafar Spain, Luis Rubiales, daga harkokin kwallon kafa har tsawon shekaru uku, na nazarin yadda za a tsaurara masa takunkumi.

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Spaniya, Luis Rubiales  kenan.
Tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Spaniya, Luis Rubiales kenan. REUTERS - DENIS BALIBOUSE
Talla

Rubiales mai shekaru 46, an dakatar da shi ne a watan Oktoban da ya gabata, sakamakon samunsa da laifi mai kama da cin zarafi, bayan kammala gasar cin kofin duniya ta mata ta 2023.

Dakataccen shugaban, ya yiwa ‘yar wasan tsakiyar Spain, Jenni Hermoso sumba, lokacin da ‘yan wasan ke karbar lambar yabo, bayan kammala gasar da Spaniya ta samu galaba akan Ingila da ci daya da nema.

A watan Satumba ne Rubiales ya ajiye aikinsa, bayan an dauki makonni ana kai ruwa rana da shi kan ya ajiye aikinsa, sakamakon zargin aikata ba daidai ba a matsayinsa na shugaba.

Abin da kwamitin ladaftarwa na Fifa ya ce, a matsayinsa na shugaba da ke rike da babban mukami, abin da aka tsammata daga wurinsa shine, ya kama mutuncinsa da kuma kare mutuncin mata ‘yan wasa

Daga cikin dalilan da ya sanya kwamitin dakatar da shi tsawon shekaru uku kuwa akwai:

  • Rashin fitowa bainar jama’a ya nemi gafara
  • Rubiales ya dage kan cewa, sumbatar Hermoso da ya yi ba wani abu ne maras kyau ba, karshe ma sai ya rika kiran masu sukarsa da sunan sakarkaru.
  • Sakon da aka wallafa a shafin hukumar kwallon kafar Spain da sunan Hermono, amma kuma ba ita ce ta rubuta ba.
  • Amfani da hukumar kwallon kafar ta Spain wajen kare kansa, tare da yin watsi da waccar tuhuma ta sumba da ake masa.
  • Matsawa wannan ‘yar wasa a wurare da dama, da zarar sun hadu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.