FIFA ta haramta wa Rubiales shiga harkokin wasanni na tsawon shekaru 3
FIFA ta yanke hukuncin haramta wa tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Spain Luis Rubiales shiga harkokin wasanni a tsawon shekaru 3, saboda sumbatar ‘yar wasa Jenni Hermoso da ke cikin tawagar kasarsa da ta lashe gasar cin kofin duniya ta mata.
Wallafawa ranar:
Hukumar kwallon kafar ta duniya ta ce hukuncin ya hau kan Rubiales ne saboda samunsa da laifin karya dokokinta na da’a.
A baya dai, dakatarwar kwanaki 90 FIFA ta yi wa tsohon shugaban hukumar kwallon kafar ta Spain, akan sumbatar da ya yi wa Jenni Hermoso ba da son ranta ba, kamar yadda ‘yar wasan ta bayyana, sa’o’i bayan aukuwar lamarin.
Har zuwa lokacin da yayi murabus Rubiales ya ci gaba da musanta zargin da ake masa, inda ya ce a bisa son ran ‘yar wasan ta Spain ya sumbace ta baki da baki.
Da farkon faruwar lamarin Rubiales ya gagguta neman afuwar Jenni Hermoso da sauran mutane, inda ya ce farin ciki ne ya ingiza shi wuce gona da iri, kodayake ya ce ‘yar wasan ba ta dauki batun da zafi ba.
Sai dai ba da jimawa ba, ‘yar wasan ta kira taron manema labarai, inda ta musanta ikirarin shugaban nata, lamarin da ya sanya hukumar kwallon kafar Spain ta yi barazanar daukar matakin shari’a kanta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu