Isa ga babban shafi

FIFA ta jajantawa Diaz kan garkuwa da mahaifansa

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Gianni Infantino, ya mika sakon jajantawa da kuma addu’a ga dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafar Liverpool Luis Diaz, da wasu 'yan bindiga suka yi garkuwa da mahaifansa a Colombia.

Futebol. Imagem de Arquivo.
Futebol. Imagem de Arquivo. © AFP - YASIN AKGUL
Talla

Itama hukumar kwallon kafar kasar ta Colombia ta fidda wata sanarwar a shafinta na X da aka fi sani da Twitter, inda ta bukatar wadanda suka yi garkuwa da mahaifin dan wasan su gaggauta sakinsa ba tare da bada wani zabi ba.

Jami’an tsaron kasar sun sanar da kubutar da mahaifiyar Diaz, inda sojoji da kuma ‘yan sanda ke ci gaba da farautar wadanda suka yi garkuwa da mahaifinsa don kubutar da shi.

Bayan tashi daga wasan da Liverpool ta yi nasara da ci 3 da nema a gida kan Nottingham Forest, mai horas da kungiyar Jurgen Klopp ya ce shirya yadda wasan ya gudana shi ne mafi wahala da ya taba fuskanta, sabida abinda ya faru da dan wasansu.

Bayan jefa kwallon da Diogo Jota ya rike rigar Nottingham Forest, ya da ga rigar Diaz mai lamba 7, a matsayin nuna goyon bayansu gareshi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.