Isa ga babban shafi

AC MILAN ta kulla kwantragi da dan wasan gaban Najeriya Samuel Chukwueze

AC Milan ta sanar da kulla kwantragi da dan wasan gaban Najeriya Samuel Chukwueze wanda a baya ya kasance da kungiyar Villarreal ta kasar Spain.Labarin daga kungiyar  ta Ac Milan da ke rukunin kungiyoyi dake cikin  gasar Serie A na kasar  Italia,na nuna farin cikin kungiyar bayan daukar Samuel Chimerenka Chukwueze daga Villarreal CF.

Dan wasan Najeriya Samuel Chukwueze
Dan wasan Najeriya Samuel Chukwueze AFP
Talla

Dan wasan na Najeriya ya kulla yarjejeniya da Rossoneri har zuwa ranar 30 ga Yuni, 2028.

Tarihi ya nuna cewa an haife shi a Umuahia dake jihar Abia a  tarrayar Najeriya a ranar 22 ga Mayu shekarar 1999.

 Samuel ya zo ta bangaren matasa na Kwalejin Kwallon Kafa ta Diamond kafin ya koma Villarreal a 2017, kamar yadda aka bayyana a shafukan sada zumunta.

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Samuel Chukwueze
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Samuel Chukwueze NAN

Ya soma da yan aji farko na kungiyar  ta Spain, ya buga wasanni 20 kuma ya zura kwallaye hudu kafin ya fara buga wasa da babbar kungiyarsa. Samuel Chukwueze ya zabi riga mai lamba 21.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.