Isa ga babban shafi

Croatia ta kai wasan karshe a gasar Nations League bayan doke Holland

Nasara daya  tal ta ragewa Croatia samun damar dage kofin gasar lid din kasashen Turai bayan doke Netherland mai masaukin baki a wasan gab da na karshe da suka hadu a jiya laraba.

Tawagar 'yan wasan Croatia.
Tawagar 'yan wasan Croatia. AP - Petr David Josek
Talla

An dai ta shi wasan kwallaye 2 da 4, kuma mai masaukin baki ta fara zura kwallo ta hannun Donyell Malen a minti na 34 da fara wasa har zuwa dawowa daga hutun rabin lokaci kuma Netherlands din ke jagoranci gabanin fenaritin da Croatia ta samu ta hannun dan wasanta Kramaric.

Bayan da Croatia ta samu damar yin kunnen doki ne kuma ta kara kaimi a wasan inda Pasalic ya zura kwallo ta biyu a minti na 72 kana yayinda Noa Lang na Dutch ya farke wannan kwallo a minti na 90 amma kuma Bruno Petkovic ya kara a minti na 98 gabanin fenaritin Modric da ya bai Croatia gagarumar nasara.

Nasarar ta Croatia na nuna cewa za ta hadu da ko dai Italy ko kuma Spain a wasan karshe na gasar ta Nations League lura da yadda kasashen biyu ke Shirin haduwa anjima da daddare don tantance wadda za ta yi nasara don kaiwa wasan na karshe.

Duk da rashin nasarar da Netherlands za ta shirya fafatawa don neman gurbin ta 3 wanda itama za ta doka da ko dai Italiyan ko kuma Spain ya dai danganta da wadda ta sha kaye cikin a haduwar ta yau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.