Isa ga babban shafi

Manchester United za ta iya doke kowacce kungiya a Europa- Erik Ten Hag

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United Erik Ten Hag ya ce a yanzu kungiyar ba ta shakkar haduwa da duk kowacce kungiya, bayan da ta doke Barcelona da kwallaye 2-1 a gasar Europa jiya alhamis wanda ya ba su damar kai wa zagayen ‘yan 16 na gasar. 

'Yan wasan Manchester United.
'Yan wasan Manchester United. © REUTERS/Craig Brough
Talla

Dan wasan gaba na Barcelona Robert Lewandowski ne ya fara jefa kwallo a wasan bayan samun bugun daga kai sai mai tsaron gida, amma bayan dawowa hutun rabin lokaci Fred ya farke wa United sannan kuma Antony ya kara kwallo ta biyu. 

Ten Hag ya bayyana nasarar ta su a matsayin gagaruma, domin a cewar sa duk kungiyar da za ta iya doke Barcelona ba bu wata kungiya da ba za ka iya doke ta ba. 

Wasa 18 ke nan rabon da a doke United a filin ta na Old Trafford, lamarin da ke nuna irin karfin da tawagar ke samu a karkashin Ten Hag. 

Ita kuwa Barcelona duk da jagorantar gasarar Laliga da ta ke yi a bana, amma tawagar ta Xavi Hernandez ba ta tabuka katabus a duk wata gasa da ta shafi Turai, domin ko a wasannin ta na rukuni a gasar zakarun Turai kashi ta sha a hannun Bayern Munich da kuma Inter Milan. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.