Na gama da nahiyar Turai - Ronaldo
Cristiano Ronaldo ya ce aikinsa ya kare a Turai, amma ya samu damammaki da dama daga wasu kungiyoyi kafin ya koma kungiyar Al Nassr ta Saudiyya.
Wallafawa ranar:
Ya koma Al Nassr ne bayan ya bar Manchester United bayan wata tattaunawa mai cike da cece-kuce inda ya soki manufofin kungiyar.
Kyaftin din na Portugal, mai shekaru 37, ya ce ya samu tayi daga kungiyoyi a Brazil, Australia, Amurka da Portugal.
Rahotanni sun ce Ronaldo na shirin karbar albashi mafi girma a tarihin duniyar kwallon kafa kan sama da yuro miliyan 177 a duk shekara a yarjejeniyar da za ta kare har zuwa shekarar 2025.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu