Isa ga babban shafi

Ronaldo zai fara bugawa Al Nassr wasa a watan Janairu

Fitaccen dan wasan kwallon kafa na kasar Portugal, Cristiano Ronaldo zai fara buga wa kungiyar Al Nassr ta kasar Saudiyya wasa daga ranar 1 ga watan Janairun 2023, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar Sipaniya suka ruwaito.

Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo © Managing Madrid
Talla

Dan wasan na kasar Portugal zai takawa kungiyar leda kan kwantiragin shekaru biyu da rabi, a cewar wani rahoto da jaridar MARCA ta kasar Sipaniya ta fitar.

Kafin shekarar ta kare, dan wasan mai shekaru 37 ya shirya amincewa da kwantiragin dala miliyan 217 a duk shekara.

Ronaldo ya kawo karshen dangantakarsa da Manchester United kwanaki kadan kafin gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar, wanda hakan ya ba shi damar tattaunawa da kowace kungiya.

Duk da ikirarin cewa zai samu kungiyoyi a gasar cin kofin zakarun Turai da za su saye shi, Al-Nassr ce ta fi nuna sha'awa tun daga farko.

Ronaldo ya dade yana fatan ci gaba da zama Turai, amma sabon kwantaragin zai sanya dan wasan na kasar Portugal kasancewa wanda ya fi karbar albashi a duniya. .

Jimlar kudin da kwantiragin Ronaldo da Al Nassr ya nuna, zai kusan Euro miliyan 200 a duk kakar wasa, in ji jaridar MARCA.

A halin yanzu Lionel Messi da Neymar a Paris Saint-Germain ne ke kan gaba, ko da yake Yuro miliyan 75 da 70 da suke samu a duk kakar wasa ya yi kasa da abin da Cristiano zai karba a Saudiyya.

Ronaldo zai samu kansa a kungiyar da ke neman dawo da karsashinta da ya yi rauni a gasar, inda ya kasance akwai tazara tsakaninta da manyan kungiyoyi na duniya.

Kasancewar David Ospina shima, wato mai tsaron ragar Colombia kwantiraginsa ya kare a Napoli ya yanke shawarar amincewa da tayin Saudiyya a kaka mai zuwa.

Kafin gasar cin kofin duniya ta 2022 a Qatar, Al Nassr ta nuna sha’awar sayo Ronaldo, amma ya ki cewa komai saboda ya mayar da hankali kan rawar da kasarsa za ta taka a gasar.

Rahotanni sun bayyana cewa, Ronaldo da iyalansa na Dubai  yanzu haka, inda suke dakon tabbatar da kwantaragin, wanda kuma ya hada da yarjejeniyar tallace-tallace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.