Isa ga babban shafi

Brazil ta lallasa Koriya ta Kudu inda za ta buga wasanta na gaba da Croatia

Brazil ta nuna dalilin da ya sa ta zama ta fi kowace kungiya a duniya bayan da ta lallasa Koriya ta Kudu a farkon rabin lokaci, inda ta ci hudu a cikin mintuna 36 na farko.

Wasan zagayen 'yan 16 da Brazil ta kara da Koriya ta Kudu kenan
Wasan zagayen 'yan 16 da Brazil ta kara da Koriya ta Kudu kenan REUTERS - CARL RECINE
Talla

Ko da yake Koriya ta Kudu farke kwallo daya a zagaye na biyu, daga Paik Seung-ho.

Yanzu haka dai, Brazil za ta fafata da Croatia a ranar Juma'a a wasan kusa da na karshe.

An nuno yadda 'yan wasan Brazil ke rike da tuta da ke ambaton Pele, fitaccen dan wasan Brazil wanda a halin yanzu ke kwance a asibiti.

Pele ya kafa kasance dan wasan da ya fi kowa zura kwallo a raga a Brazil, inda Neymar, ya ci kwallaye 76, kwallo daya kacal a bayansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.