Isa ga babban shafi

Ghana ta sha da kyar a hannun Koriya ta Kudu

Kwallaye biyu da Mohammed Kudus ya jefa tare da guda da Mohammed Salisu ya zira a karawar da Ghana ta yi da Koriya ta Koriya sun taimaka mata samun nasara a ci gaba da wasannin cin kofin duniyar da ke gudana a kasar Qatar.

Yadda wasan Ghana da Koriya ta Kudu ya kaya
Yadda wasan Ghana da Koriya ta Kudu ya kaya REUTERS - MOLLY DARLINGTON
Talla

Wannan gagarumar nasarar ta farfado da damar da Ghana ke da ita ta zuwa zagaye na gaba, muddin kasar ta samu nasara a wasanta na karshe da za ta fafata da Uruguay.

Mohammed Salisu ya fara jefawa Ghana kwallo a wasan, yayin da Kudus ya jefa ta biyu a zagaye na farko.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, Koriya ta Kudu ta farke ci biyun ta hannun dan wasanta Cho Gue-sung, abin da ya jefa fargaba tsakanin magoya bayan kasar Ghana.

A minti na 68 Mohammed Kudus ya jefa kwallo ta 3, abin da ya bai wa Ghana nasara, duk da yake 'yan kasar Koriya ba su yi kasa a gwiwa ba, sakamakon munanan hare-haren da suka yi ta kai wa har zuwa lokacin tashi a wasan.

Yanzu haka Ghana na da maki 3 a teburi, a matsayi na biyu, yayin da Portugal ke sahun gaba da maki 3, kafin karawar da za ta yi da Uruguay a yammacin yau.

Ganin irin wadannan munanan hare-hare, hankalin magoya bayan Ghana ya tashi, musamman yadda alkalin wasa ya kara mintina 10 kafin ya tashi wasan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.