Isa ga babban shafi

Yadda Faransa ta lallasa Australia a gasar cin kofin duniya

Olivier Giroud ya kafa irin tarihin da Thierry Henry kafa,  matsayin dan wasan Faransa da ya fi zura kwallo a raga da kwallaye biyu, bayan da kasar ta doke Australia da ci 4-1, sannan kuma ta samu nasarar kare martabarta a gasar cin kofin duniya na ranar Talata.

Yadda Faransa ta lallasa Australia
Yadda Faransa ta lallasa Australia REUTERS - MOLLY DARLINGTON
Talla

Australia ce dai ta fara zura kwallo a ragar faransa a filin wasa na Al Janoub cikin mintuna tara kacal da fara wasan daga Craig Goodwin.

Adrien Rabiot ya farke kwallon, kafin Giroud ya zura ta biyu cikin dakika 32 da fara wasan a zagayen farko.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne, Kylian Mbappe ya zura kwallo ta uku, yayin da  Giroud ya cike ta hudun, wanda hakan ne ya bashi damar kamo dan wasan Faransa Henry da ya zurawa kasarsa kwallaye 51.

Samun nasara a wasan dai ya bawa Faransa damar kasancewa jagora a saman teburin D, bayan abokan hamayyarta Denmark da Tunisia sun tashi a nasu wasan babu ci a birnin Doha.

Yana da shekaru 36, tsohon dan wasan AC Milan Giroud, wanda ya buga wasanni 115, shi ne dan wasa mafi tsufa da ya ci wa Faransa kwallo a gasar cin kofin duniya.

Amma duk da haka kusan babu tabbas na takawa kasar leda, idan har Karim Benzema ya samu damar bugawa.

A maimakon haka, janyewar gwarzon dan wasan Ballon d’Or da ya samu rauni a cinyarsa a jajibirin gasar, ya bawa Giroud damar shiga tawagar, wanda ya kasance babban dan wasa ga koci Didier Deschamps a gasar cin kofin duniya na 2018 da Faransa ta dauki kofin gasar a kasar Rasha, amma bai zura kwallo a raga ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.