Isa ga babban shafi

Seria A ta ci tarar Verona yuro dubu 12 kan nuna wariya ga Victor Osimhen

Bayan kaddamar da bincike kan cin zarafin dan wasan Najeriya Victor Osimhen da wasu magoya bayan Hellas Verona suka yi, hukumar ladabtarwa ta Seria A ta Italiya ta ci tarar kungiyar kwallon kafar kudi Yuro dubu 12,000.

Victor Osimhen dan wasan kungiyar Napoli dake gasar Seria A.
Victor Osimhen dan wasan kungiyar Napoli dake gasar Seria A. AP - Alessandro Garofalo
Talla

Napoli ta yi tattaki zuwa gidan Hellas Verona ne a ranar Litinin don buga wasanta na farko na gasar Seria A ta bana, wanda daga karshen Napolin ta samu nasara da kwallaye 5-2.

Yayin da ake tsaka da fafata wasan ne, wani sashi na magoya bayan Veronan suka rika rera wakoki da kuma yin kukan biri ga dan wasan Osimhen dan Najeriya.

Sai dai ko alama dan wasan bai nuna damuwa ba, inda shima daga bisani ya rama abinda aka yi masa ta hanyar nuna kamar yana kuka a na’urar kamara bayan da ya ci kwallo ta biyu ya kuma taimaka wajen jefa ta 5 a ragar masu masaukin bakin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.