Isa ga babban shafi

United ta nanata cewa bata shirya sayar da Ronaldo ba

Cristiano Ronaldo ya shaidawa Manchester United cewa yana son sauya sheka domin samun damar buga gasar zakarun Turai amma United ta sake nanata cewa bata shirya siyar da dan wasan na Portugal mai shekara 37 ba.

Christiano Ronaldo ya ce yana da burin buga gasar zakarun Turai a bana
Christiano Ronaldo ya ce yana da burin buga gasar zakarun Turai a bana © AFP - OLI SCARFF
Talla

A gefe guda kuma har yanzu United din na fatan siyan dan wasan tsakiyar Netherlands Frenkie de Jong daga Barcelona.

Amma De Jong ya shaida wa takwarorinsa na Barca cewa ba shi da niyyar barin Camp Nou a bana, duk da zawarcin da United din ke yi.

Bugu da kari sabon dan wasan Manchester United Lisandro Martinez yanzu shine dan wasan baya mafi gajarta a gasar Premier kakar wasa mai zuwa, bayan da ya koma kungiyar daga Ajax a kan kudi Yuro miliyan 67.5.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.