Isa ga babban shafi

Har yanzu Madrid ce kungiya mafi daraja a Turai - Rahoto

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta ci gaba da zama kungiyar kwallon kafa mafi daraja a nahiyar turai duk da yadda ake kara samun ci gaba a gasar firimiya ta kasar Ingila. Kamar yadda wani rahoto da Mujallar Football Benchmark ta wallafa ranar Alhamis.

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta ci gaba da zama kungiyar kwallon kafa mafi daraja a nahiyar turai duk da yadda ake kara samun ci gaba a gasar firimiya ta kasar Ingila.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta ci gaba da zama kungiyar kwallon kafa mafi daraja a nahiyar turai duk da yadda ake kara samun ci gaba a gasar firimiya ta kasar Ingila. © Real Madrid
Talla

Rahoton ya bayyana manyan kungiyoyin Turai 32, inda aka yi la’akari da kimarsu bisa kasafin kudadensu na shekara da kuma kimar kungiyar.

Gasar Zakarun Turai

Real, wacce za ta kara da Liverpool a wasan karshe na gasar cin kofin zakarun Turai a ranar Asabar, ta zo kan gaba a karo na hudu a jere na rahoton, da darajar kudi Kusan dala biliyan 3.5.

Duk da haka bata kai yadda take a shekarar 2020 wato kafin barkewar cutar korona ba, inda dake da sama da Yuro biliyan 3.5.

Marubucin rahoton Andrea Sartori ya ce "Real Madrid ta ci gaba da rike matsayin ne saboda ci gaba da samun nasara a wasanni da kuma harkokin kasuwanci."

Asara saboda korona

Ya ce duk da haka kungiyar  ta yi asarar Yuro miliyan 84 sakamakon rashin samun kudaden shiga na ranar wasa saboda rashin halartan magoya bayanta filin wasa saboda barkewar cutar korona.

Barcelona

Manchester United ke matsayi na biyu da Yuro biliyan 2.9, Barcelona da Bayern Munich ke matsayi na uku da na hudu da Yuro miliyan 2.8 , sai Liverpool ta biyar da sama da Yuro biliyan 2.556.

Daga cikin kungiyoyi 32 mafi daraja, hudu ne kawai wato Ajax da Galatasaray da Porto da kuma Benfica ne basa cikin manyan kungiyoyin Turai biyar ba, wato na  Ingila, Spain, Jamus, Italiya da Faransa.

Yayin da goman farko suka fito daga Ingila, a daidai lokacin da kungiyoyin gasar Premier suka mamaye wasannin Turai.

Rahoton ya kara da cewa "Abin da ke kara martabar kungiyoyin Ingila zuwa ga daukaka ita ce nasarar da suka samu a bangaren kudi."

"Jimillar kudaden shiga da gasar Premier ta samu ya kai  Euro biliyan 5.1, amatsayin wadda ta fi ko wanne.

PSG

Paris Saint-Germain ta samu ci gaban cikin shekaru bakwai tun bayan rahoton farko na Football Benchmark, wanda ya karu da kashi 153, wato Karin sama da Yuro biliyan biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.