Isa ga babban shafi

Tsohon dan wasan Ajax ya mutu bayan dukan da ya sha a hannun 'yan uwansa

Dan wasan kasar Jamhuriyar Congo Jody Lukoki da ya fara buga kwallon kafa ajin kwararru daga kungiyar Ajax ya mutu yana da shekaru 29.

Dan wasan Jamhuriyar Congo marigayi Jody Lukoki.
Dan wasan Jamhuriyar Congo marigayi Jody Lukoki. FABRICE COFFRINI / AFP
Talla

Bayanan da jaridu da dama suka ruwaito ciki har da Jaridar Het Parool da ke kasar Netherlands, sun ce kafin mutuwarsa, Lukoki yayi fama da ciwon zuciya ne a wani asibiti da ke garin Almere, sakamakon dukan kawo wukar da wasu ‘yan uwansa suka lakada masa, a dalilin wata takaddama da suka yi.

Kungiya ta karshe da Lukoki ya bugawa itace ta FC Twente da ke kasar Holland ko Netherlands, wadda ya kulla yarjejeniya da ita a cikin watan Yunin da ya gabata, sai dai tun daga waccan lokacin bai samu bugawa kungiyar wasa ba, saboda mummunan raunin da ya ji a gwiwarsa, yayin da yake atisayen sharar fage.

Kafin kulla yarjejeniya da FC Twente, daga cikin kungiyoyin da Lukoki ya bugawa akwai Ajax, da SC Cambuur, da kuma Yeni Malatyaspor.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.