Isa ga babban shafi
Wasanni-Tennis

Djokovic ya yi nasara a kotu kan hana shi doka gasar Australian Open

Zakaran kwallon Tennis na Duniya Novak Djokovic ya yi nasara gaban kotu game da karar da ya shigar kan hana shi damar haskawa a gasar Australian Open da hukumomin Australia suka yi baya ga tsare shi a hannun hukumar kula da shige da ficen kasar.

Wata zanga-zangar bukatar sakin Djokovic da magoya bayansa suka gudanar.
Wata zanga-zangar bukatar sakin Djokovic da magoya bayansa suka gudanar. FLORIAN WIESER APA/AFP
Talla

Hukuncin kotun karkashin jagorancin alkali Anthony Kelly ya bayyana tsarewar da hukumomin Australia suka yiwa Djokovic a matsayin abin da ya sabawa ka’ida.

Hukuncin ya bukaci gaggauta sakin zakaran na Tennis lamba daya tare da bashi damar haskawa a gasar wadda za ta faro cikin watan nan.

Sai dai duk da hukuncin kotun lauyan gwamnati Chrisopher Tran ya ce za su amfani da karfin ikon da suke da shi wajen haramtawa Djokovic damar shiga kasar har na shekaru 3.

Matakin tsare Novak Djokovic dan Serbia mai shekaru 34 dai ya haddasa cece-kuce tare da kakkarfar zanga-zangar magoya bayansa musamman a kasarsa da kuma Australia wadan ke kiraye-kirayen bukatar sakin shi.

Tun farko hukumomin Australia suka sahalewa Djokovic damar shiga kasar tare da bashi Visa duk da kasancewarsa wanda ya yi fama da coronavirus a baya ba kuma tare da karbar rigakafin cutar ba, amma kuma bayan isarsa aka damkeshi saboda gaza nuna shaidar allurar.

Za dai a faro gasar ta Australian Open a ranar 17 ga watan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.