Isa ga babban shafi
Wasanni - kwallon kafa

EUFA ta jaddada matakin ladaftarwa kan kungiyoyi da ke goyon bayan Super League

Hukumar kula da wasan kwallon kafar Turai UEFA a ta fara daukan matakin ladabtarwa kan kungiyoyi uku da har yanzu suka ki yin watsi da Shirinsu na neman shirya gasar European Super League ba, da suka hada da Real Madrid da Barcelona da kuma Juventus.

Alamar gasar Super League mai cike da cece kuce
Alamar gasar Super League mai cike da cece kuce REUTERS - DADO RUVIC
Talla

A kokarin daukar matakin UEFA ta nada sifetocin ladabtarwa don gudanar da bincike game da yiwuwar keta dokokin UEFA da kungiyoyin suka yi "dangane da gasar ta 'Super League'," dake neman zama kishiya  ga Champions League.

Hukumar tace "Za a ci gaba da Karin bayani game da wannan batun a lokacin da ya dace."

UEFA a makon da ya gabata ta ce za ta dauki "matakin da ya dace" a kan kungiyoyi uku da har yanzu ke goyon bayan shirin Super League, gasar da za ta tabbatar da mambobin da suka kafa ta shiga a kowane kakar wasa, ba tare da sunyi wasan neman gurbi ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.