Isa ga babban shafi
Wasanni

Hakar Arsenal ta gaza cimma ruwa

Chelsea ta lashe kofin gasar Europa a jiya laraba, bayan lallasa Arsenal da 4-1, a wasan karshe da suka fafata a filin wasa na Baku, babban birnin kasar Azerbeijan.

Yan wasan Chelsea yayin murnar lallasa Arsenal a wasan karshe na gasar Europa.
Yan wasan Chelsea yayin murnar lallasa Arsenal a wasan karshe na gasar Europa. REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

A zangon farko na fafatawar kungiyoyin biyu babu wadda ta jefawa wata kwallo a raga,har aka tafi hutun rabin lokaci. Bayan dawowa zango na biyu ne Olivier Gioud ya jefa kwallon farko a ragar Arsenal, Pedro da Eden Hazard suka kara jefa wasu kwallayen 2, daga bisani kuma dan wasan Arsenal Alex Iwobi ya rama kwallo guda.

Kafin kammala wasan dai Hazard da ke bankwana da Chelsea ya sake jefa Karin kwallo aragar Arsenal lamarin da yasa kenan aka kammala wasan na jiya 4-1.

Kafin wasan karshen na gasar Europa dai, tuni Chelsea ta samu tikitin halartar gasar zakarun Turai mai zuwa, yayinda ita kuwa Arsenal ke neman nasarar lashe kofin na Europa domin samun damar zuwa gasar ta Zakarun Turai, to amma hakan bata samu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.