Kwallon kafa
Blanc zai bar PSG
Rahotanni daga Faransa sun ce Kocin Paris Saint Germain Laurent Blanc zai kawo karshen horar da kungiyar a cikin wannan makon, kamar yadda wakilin shi ya tabbatarwa tashar rediyon Europe 1 a jiya Litinin.
Wallafawa ranar:
Talla
Jean-Pierre Bernes ya ce yanzu suna tattaunawa da PSG kan makomar kocin wanda ya lashe wa kungiyar kofuna 6 a kaka biyu.
Rahotanni daga Spain sun ce PSG na tattaunawa da kocin Sevilla Emery domin maye gurbin Blanc.
PSG dai ta shiga neman sabon koci ne tun lokacin da Manchester City ta fitar da ita a gasar cin kofin zakarun Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu