Isa ga babban shafi
UEFA

Barcelona ta lashe Super Cup

Barcelona ta lashe Super Cup na Turai bayan ta sha da kyar ci 5 da 4 a fafatawar da suka yi da Sevilla a daren jiya Talata. Kwallaye hudu Barcelona ta jefa kafin daga bisani Sevilla ta rama kwallayen, dalilin da ya sa aka kara minti 30.

Barcelona ta doke Sevilla a fafatawar da suka yi a Super Cup a  Dinamo Arena da ke Tbilisi a Georgia
Barcelona ta doke Sevilla a fafatawar da suka yi a Super Cup a Dinamo Arena da ke Tbilisi a Georgia REUTERS/David Mdzinarishvili
Talla

Ana dab da zuwa bugun fanariti ne, Allah ya taimaki Barcelona, Pedro ya jefa kwallo a raga da ya ba kungiyar nasarar lashe babban kofin na Turai a jiya.

Yanzu Barcelona ta kara kofin ga jerin kofuna uku da ta lashe a kakar da ta gabata.
Ana fafatawar lashe Super cup na Turai ne dai tsakanin kungiyar da ta lashe kofin zakarun Turai da kuma Europa League.

Nan gaba Barcelona da ta lashe La liga za ta kara da Athletic Bilbao da ta lashe Copa del Ray domin neman lashe kofin Super na Spain.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.