Isa ga babban shafi
Premier League

Chelsea ta lallasa Tottenham

Kungiyar Chelsea ta lallasa Tottenham ci 3 da 0, yayin da kuma Manchester City ta casa Sunderland ci 1 da 0, Arsenal kuma ta doke Southampton ci 1 da 0 a wasannin da manyan  kungiyoyin na Ingila suka fafata a ranar Laraba.

Dan wasan Chelsea Didier Drogba
Dan wasan Chelsea Didier Drogba REUTERS/Phil Noble
Talla

Yanzu maki biyu ne ke tsakanin Manchester United da ke matsayi na hudu da kuma Arsenal.

Ana dab da kammala wasa ne Alexis Sanchez ya jefa wa Arsenal kwallo a ragar Southampton da ke matsayi na uku a teburin Premier.

Kuma yanzu maki guda ne tsakanin Southampton da Manchester United kafin su fafata da juna a ranar Litinin mai zuwa.

Tuni Manchester United ta doke Stoke City ci 2 da 1 a ranar Talata, kamar yadda Liverpool ta ba Leicester kashi ci 3 da 1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.