Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Argentina da Belgium sun tsallake rijiya da baya

Kasar Argentina ta doke Switzerland da ci 1-0 inda yanzu haka ta samu shiga zagayen quarter finals yayin da Belgium ta kawar da kasar Amurka a gasar cin kofin duniya.

Messi da Di Maria suna murnar zira kwallo a ragar Switzerland
Messi da Di Maria suna murnar zira kwallo a ragar Switzerland REUTERS/Ivan Alvarado
Talla

An dai kwashe mintina 90 bangarorin Argentina da Switzerland ba su samu nasarar zira kwallaye ba, sai bayan da ya rage mintina biyu daga cikin karin lokacin da aka yi, Argentinan ta samu lagwan Switzerland, inda Angel Di Maria ya zira kwallon da Lionel Messi ya yi hidimar wajen samar da ita.

Hakan kuma ya sa Messin ya samu lambar yabo, a matsayin dan wasan da yafi haskawa a wasan a karo na hudu a wannan gasa.

Yanzu kuma Argentina za ta kara ne da kasar Belgium wacce itama ta samu galaba akan Amurka da ci 2-1 a jiya, bayan suma da aka samu karin lokaci yayin da bangarorin biyu suka kasa zira kwallaye a lokutan farko.

Rabon dai da Belgium ta samu shiga zagayen quarters finals a wannan gasa, tun shekaru 28 da suka gabata.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.