Europa League: An yi waje da Tottenham
A gasar europa league ta Turai Benfica ta yi waje da Tottenham a gasar Europa League bayan sun tashi ci 2-2 a daren Alhamis, kuma Benfica ta tsallake zuwa zagayen kwata Fainal da jimillar kwallaye ci 5-3. A karawa da aka yi tsakanin kungiyoyin Italiya guda biyu, Andrea Pirlo ne ya taimakawa kungiyar Juventus doke Fiorentina da ci 1-0, Juve ta tsallake ne da jimillar kwallaye ci 2-1.
Wallafawa ranar:
Wasa tsakanin tsakanin FC Porto da Napoli an tashi ne ci 2-2, amma Porto ce ta tsallake da jimillar kwallaye ci 3-2.
Lyon ta yi waje ne da Viktoria Pilsen ta Jamhuriyyar Czech da jimillar kwallaye ci 5-3.
A bugun daga kai sai mai tsaron gida ne Sevilla ta doke Real Betis ci 4-3 bayan Sevilla tarama dukan da Betis ta yi mata ci 2 a karawa ta farko.
A yau Juma’a ne dai za’a hada kungiyoyin da zasu kara a zagayen kwata Fainal tare da kungiyoyin da zasu kara a kwata Fainal a gasar zakarun Turai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu