Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Neymar ya murmure daga raunin da ya ji

Likitocin kungiyar Barcelona sun tabbatar da cewa dan wasansu Neymar ya murmure daga raunin da yaji, wanda hakan ake sa ran zai bashi damar karawa a wasannin da za a yi a gasar La Laiga na karshen mako da kuma karawar da Barcelonan za ta yi da Manchester City a ranar Talata mai zuwa a gasar Zakarun Turai ta Champions League.

Dan wasan Barcelona, Neymar
Dan wasan Barcelona, Neymar REUTERS/Gustau Nacarino
Talla

Rahotanni sun ce a yau juma’a an yi atisaye tare da Neymar, kuma a cewar mai horar da ‘yan wasan, wato Gerardo Martino, Neymar ya yi atisaye da su cikin koshin lafiya.

Shi dai Neymar ya samu raunin ne a watan da ya gabata a gasar Copa Del Rey, yayin da suke karawa da Getafe.

A karshen makon nan Barcelona za ta kara ne da Rayo Vallecano wacce ke kasan taburin gasar yayin da ita kuma Barcelona ke saman teburi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.