Isa ga babban shafi
Premier

QPR ta samu sa’ar Chelsea, Liverpool ta lallasa Sunderland

Kungiyar Chelsea ta sha kashi ci 1-0 a hannun QPR a Stamford Bridge, kuma Tsohon dan wasan kungiyar ne Wright-Phillips ya zira kwallon a ragar Chelsea ana saura minti 12 a kammala wasa.

'Yan wasan QPR suna murnanr lashe wasansu da Chelsea
'Yan wasan QPR suna murnanr lashe wasansu da Chelsea
Talla

Kocin kungiyar QPR da ke can kasan Tebur Harry Redknapp, yace doke Chelsea haske ne ga ci gabansu a farkon shekara.

Wannan ne dai karo na Biyu da QPR ta samu nasarar lashe wasa tun fara kakar wasa a bana.

Kungiyar Newcastle United kuma ta bude wa Chelsea kofar fara tattaunawa game da mallakar dan wasanta Demba Ba na Senegal.

Ana sa ran Chelsea zata saye dan wasan akan kudin da suka kai Euro Miliyan 8.6.
A daya bangaren kuma Everton ta lallasa Newcastle United ci 2-1 a kokarin da Eveton din ke yi domin samun hurumin buga gasar zakarun Turai.

Liverpool kuma ta doke Sunderland ne ci 3-0 a Anfield wanda ya bata damar haurowa zuwa matsayi na 8 a Teburin Premier.

Wannan kuma na zuwa ne bayan kungiyar ta Liverpool ta kammala kulla yarjejeniya da dan Wasan Chelsea Daniel Sturridge a matsayin dan wasan Aro.

Manchester United ce dai saman Teburin Premier tazarar maki 7 tsakaninta da Manchesrter City. Sai Tottenham a matsayi na uku da tazarar maki 1 tsakaninta da Chelsea da ke a matsayi na 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.