Isa ga babban shafi
Tennis

Nadal da Jo-Wilfried da Li na sun tsallake zagaye na uku a French Open

A wasannin Tennis gasar Roland Garos, da ake gudanarwa a Faransa Rafeal Nadal ya tsallake zagaye na uku bayan ya doke Denis Istomin dan kasar Uzbekistan. Nadal shi ne mai rike da kofin gasar kuma ya samu nasarar doke Denis ne da 6-2 6-2 6-0.

Dan kasar Spain Rafael Nadal  a karawar da ya doke  Denis Istomin, dan kasar Uzbekistan a gasar Roland Garros
Dan kasar Spain Rafael Nadal a karawar da ya doke Denis Istomin, dan kasar Uzbekistan a gasar Roland Garros REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Jo-Wilfried Tsonga dan kasar Faransa shi ma ya samu nasarar tsallakewa zuwa zagye na uku bayan ya doke Cedrik-Marcel Stebe dan kasar Jamus.

A karawa ta gaba Nadal zai kara ne da Eduardo dan kasar Argentina zuwa zagayen Quarter Final.

A bangaren mata kuma Li na ‘Yar kasar China Mai rike da kofin French Open ta doke Stephanie ‘Yar kasar Faransa kuma wannan nasarar ce ta bata damar tsallakewa zagaye na uku.

Caroline Wozniacki ma ta tsallake zagaye na uku bayan da doke Jarmila ‘Yar kasar Australia.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.