Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai - China

EU na shirin kara tallafin da take baiwa kasashe saboda hamayya da China

Hukumar Tarayyar Turai ta sanar da aniyarta ta tara kudi har Yuro biliyan 300 don zuba jari a bangaren samar da ababen more rayuwa a fadin duniya, matakin da ake gani martani ne ga shirin China na mamayar akasarin kasashen duniya ta fannin kasuwanci.

Shugabar gudanarwar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen, cikin watan Disambar 2021, lokacin da ta sanar da shirin kara tallafinsu ga kasashen zuwa Euro biliyan 300.
Shugabar gudanarwar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen, cikin watan Disambar 2021, lokacin da ta sanar da shirin kara tallafinsu ga kasashen zuwa Euro biliyan 300. © AP Photo/Olivier Matthys, Pool
Talla

Shirin da aka wa lakabi da ‘Global Gateway’ zai mayar da hankali ga tara wannan kudi a tsakanin shekarar 2021 zuwa 2027, inda zai tattaro dimbim kudade daga kasashen da ke cikin kungiyar Tarayyar Turai da cibiyoyin kudi na Tarayyar, kamar yadda wani kundi daga hukumar Tarayyar Turai ya nuna.

Ko da yake kundin bai kama sunan shirin da China ta bullo da shi ba, shugabar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta bayyana shi a matsayin wata hanya ta bunkasa zuba jari a fannin  samar da ababen more rayuwa  a fadin duniya.

China ta kaddamar shirin zuba jarinta a ababen more rayuwa da ta kira Belt and Road, a shekarar 2013, wanda ya zuwa shekarar 2020 ta zuba jarin sama da  dala biliyan 130.

Makasudin shirin shine bunkasa   hanyoyin sufuri da sadarwa a teku da tuddai da zummar hade China da Asia, Turai da Afrika don habaka kasuwanci da ci gaban kasashe, kuma ta samu dimbim abokan hulda a fadin duniya.

Sai dai kasashen yammacin Turai sun kalli hakan a matsayin wata dabara ta rinjayar kasashe masu tasowa, tana mai zargin China da ba su kwarin gwiwar karbar basukan da za su zame musu alakakai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.