Isa ga babban shafi
Turai

Guterres ya bukaci kasashen Turai su karbi bakin haure

Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci kasashen Turai da su karbi bakin haure akalla dubu dari biyu a matsayin wadanda suka cancanci samu mafaka a kasashensu.

Bakin haure sun isa garin Budapest ,Bulgaria
Bakin haure sun isa garin Budapest ,Bulgaria REUTERS/Laszlo Balogh
Talla

Wata sanarwa da ofishin hukumar ta MDD UNHCR ya fitar a wanan juma’a, ta ce alhaki ya rataya a wuyan kasashen na Turai domin karbar wadannan mutane.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wani attajirin dan kasar Masar Najib Sawari ya gabatar da shawarar neman sayar masa daya daga cikin tsibiran dake gabar ruwan kasashen Girka da Italiya, domin tsugunar da daruruwan bakin haure dake ratsa tekun medtarani suna sadaukar da rayukansu a kokarinsu na isa nahiyar turai.

Naguib Sawiris, dake harkar sadarwan zamani yace yana so kasar Girka ko Italiya ta sayar masa da wani tsibiri, da shi kuma zai nemi a samar wa yankin ‘yancin cin gashin kai, da zai tsgunar da bakin haurenm da zai samarwa ayyukan yi.

Cikin wata tattaunawa da yayi da wani gidan talibijin, Sawiris yace zai tuntubi Gwamnatocin kasashen Girka da Syria kan wannan shirin nasa, da yace yana da yakinin zai tabbata.

Ya kara da cewa akwai gomman tsibiran da babu kowa ciki, da kuma zasu iya daukar daruruwan ‘yan gudun hijira.

Attajirin yace za a iya sayen tsibiri a wadannan kasashen, kan kudin kimanin Dalar Amurka miliyon 10 zuwa miyon 100, sai dai yace muhimmin abu shine zuba jari kan ababen more rayuwa.

Fiye da mutane 2,300 ne suka mutu a kan teku, lokacin da suke kokarin tsallakawa zuwa nahiyar turai, tun cikin watan Junairu, dayawa daga cikinsu ‘yan kasar Syria, da suka tsere daga yakin basasan da aka shafe shekaru 4 da rabi ana gwabzawa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.