Yadda takunkuman ECOWAS kan Nijar ke haifawa 'yan kasa asara
Wallafawa ranar:
Kunna - 15:15
Kusan watanni uku, motoci kusan dubu biyu dauke da kayayyaki na ci gaba da kasancewa kan iyakar Nijar da Jamhuriyar Benin bisa umurnin kungiyar Ecowas. Mafi yawan motocin dai na dauke ne da kayayyakin ‘yan Nijar, yayin da wasu ke kan hanyarsu ta zuwa Mali ko kuma Najeriya, dauke da kayayyakin da ke iya lalacewa.
Shin ko akwai wata hujja da Ecowas ta dogara da ita domin hana ‘yan kasuwa da kuma masu motocin sufuri gudanar da harkokinsu na yau da kullum saboda an yi juyin mulki a wata kasa?
Wace illa wannan mataki ke iya haifar wa tattalin arzikin kasashen na Yammacin Afirka baki daya?
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin tare da Murtala Adamu...
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu