Najeriya na cikin kasashen da suka fi fama da mutuwar jarirai a duniya
Wallafawa ranar:
Kunna - 10:01
Najeriya ta kasance kasa ta biyu a jerin kasashen da ke fama da matsalar mutuwar jarirai yayin haihuwa a duniya, kamar yadda kwararru daga Cibiyar Nazarin Halittar Dan Adam ta Najeriya ta bayyana.
Kwararrun sun bayyana hakan ne a birnin Abuja yayin wani taron hadin gwiwa na masu ruwa da tsaki kan inganta shirin kula da lafiya a Najeriya bisa bayanan mutuwar jarirai da aka samu.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin Rayuwata tare da Zainab Ibrahim
Rahoton ya ce kididdigar da aka samu kan mutuwar jarirai yayin haihuwa a Najeriya ya haura kashi 46 cikin 100 a cikin 1,000 da aka haifa.
Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ya fitar da rahoton da ke nuna cewa Najeriya ta sami yawan mace-macen jarirai da kashi 42.9 a shekarar 2021, wanda hakan ya sanya ta kasance a matsayi ta biyu a tsakanin kasashen da ke da fama da wannan matsala a duniya
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu