Isa ga babban shafi
Rayuwata

Rayuwata kashi na 545 (Shirin tallafawa Mata don rage radadin rayuwa a Kaduna)

Wallafawa ranar:

Matsalar tsadar rayuwa na daya daga cikin manyan abubuwa da suka shafi duniya a halin yanzu, ba Kasashe masu tasowa kadai ba, hatta manya Kasashe masu karfin tattalin arziki, na ji a jikinsu.

Tarin Mata ke fama da matsin rayuwa a Najeriya musamman arewacin kasar ciki har da jihar Kaduna.
Tarin Mata ke fama da matsin rayuwa a Najeriya musamman arewacin kasar ciki har da jihar Kaduna. AFP PHOTO / NICHOLE SOBECKI
Talla

Akwai dai dalilai da dama da suka haifar da wannan matsala, kamar yake yake, ya haifar da annoba, haka ma matsalar fari da sauyin yanayi ma sun taka rawa wajen haifawa Kasashe matsalar tsadar rayuwa.

Najeriya, kamar sauran Kasashe masu tasowa na daga cikin jerin kasashen da jama’arsu musamman na yankunan karkara, ke fama da matsalar talauci. Hakan ne ya sanya gwamnatoci a matakai daban daban na kasar, bullo da shirye shiryen tsamo jama’a daga matsalar ta hanyar basu tallafi musamman na kudi.

A kan haka shirin rayuwata ya ziyarci jihohin Kaduna da Bauchi a Najeriya, domin jin irin gajiyar tallafin da mata suka samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
  • 10:00
  • 10:00
  • 10:00
  • 10:00
  • 10:00
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.