Isa ga babban shafi

Microsoft ba zai rufe ofishinsa na Lagos ba - gwamnatin Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta musanta rahotannin da kafafen yaɗa labarai na cikin gida suka yaɗa da ke cewa, kamfanin Microsoft zai rufe reshensa da ke birnin Lagos wanda aka kafa domin amfanar da kasashen Afrika.

Kamfanin Microsoft
Kamfanin Microsoft © 123RF
Talla

Babban Mai taimaka wa shugaban Najeriya a bangaren watsa labarai, Temitope Ajayi ne ya fitar da sanarwar da ke musanta cewa, kamfanin na Microsoft na shirin tarkata inasa-inasa domin ficewa daga ƙasar baki ɗaya.

Mista Ajayi ya ce, akwai kuskure a rahoton da kafafen yaɗa labaran suka fitar dangane da rufe ofishin na Microsoft, inda yake cewa, kamfani na samar da sauye-sauye a ayyukansa ne, amma ba wai shirin ficewa daga kasar ba.

A cewarsa, ma’aikata 30 ne kacal sabon sauyin na Microsoft zai shafe, kuma ba wai za a sallame su daga bakin aiki ba ne, face ba sauya musu matsayi.

Gwamnatin Najeriyar ta mayar da martani ne bayan labaran raɗe-raɗin rufe ofishin na Microsoft ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda hatta dan takarar shugaban ƙasa a jam’iyar Labour, Peter Obi ya wallafa jimaminsa a shafinsa na X kan wannan batu.

Obi ya bayyana cewa, ya kaɗu da sanarwar rufe ofishin na Microsoft, yana mai cewa, hakan na nuni da yadda Najeriya ke cikin bukatar gaggawa ta samar da sauye-sauyen bunkasa tattalin arzikinta.

Akwai kimanin ma’aikata 200 da ke aiki a ofishin na Microsoft da ke birnin Lagos.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.